14 Yuni 2016 - 13:57
Yan Sanda sun kashe wani dan ta'ada a Faransa

Yan Sanda a kasar Faransa sun kashe wani mutumin da ya hallaka wani jami’in dan Sanda da abokiyar zaman sa a Magnanville dake wajen birnn Paris.

Bayanai sun ce wanda ake zargin ya dabawa Dan Sanda wuka ne a gidan sa, kafin ya kutsa kai cikin gidan inda yayi garkuwa da matar dake zama da mutumin da dan su guda.

Bayan Yan Sanda sun kasa cimma yarjejeniya a tattaunawar da suka yi, sun kutsa kai gidan inda suka kashe shi.288